KASHI NA ƊAYA (SAMAR DA AIKIN YI)
Wannan rubutu raddi ne zuwa ga wasu tsirarru Kuma karnukan farautar wasu yan siyasa dake adawa da gwomnati maici a ƙoƙarin su na aibata dukkanin wani mai daraja da kima a idon jama’a muddin yana tare da gwomnati Saboda wani dalili nasu.
Mu baza mu zagi wani ko aibta wani Saboda wani ba, amma zamu zaƙulo ayyuka da kuma gudummawar da Abubakar Malami San ya bayar afannoni daban daban na rayuwar al’umma jihar Kebbi
A kashi na farko na wannan rubutu, zamu mayar da hankali ne wajen tunatar/sanar da al’umma rawar da Minista Abubakar Malami SAN ya taka kuma yake kan takawa wajen kafa mutanen jihar Kebbi a manyan Ma’aikatu Gwamnatin Tarayyar da kuma samarwa matasa ƴan asali jihar Kebbi aikin yi a wurare daban daban.
Saboda soyayyar shi ga Jihar Kebbi, Abubakar Malami SAN ya shiga ya fita dan ganin Jihar Kebbi ta samu waƙilci akowace Hukuma.
Kaɗan daga cikin nasarorin da ya samu ta wannan fanni sun haɗa da:
1. Federal Commissioner, Federal Character Commission
2. Federal Commissioner, National Population Commission
3. Federal Commissioner, Federal Civil Service Commission
4. National Commissioner, Independent National Electoral Commission
5. Managing Director, Hydro-Electric Power Producing Areas Development Commission (HYPADEC)
6. Chairman, National Commission for People with Disability
7. Director General, Legal Aid Council of Nigeria
8. Executive Chairman, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC)
9. Executive Director Finance and Administration, Sokoto Rima River Basin Development Authority (SSRBDA)
10. Executive Director Loan, Federal Mortgage Bank of Nigeria
11. Board Chairman, National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons (NAPTIP)
12. Board Chairman, Federal Medical Center (FMC) Keffi
Abubakar Malami bai manta da Matasa ba domin kuwa ya samarwa matasa fiye da ɗari shida aiki a ma’aikatun gwamnatin Tarayya da suka haɗa da
1. National Drugs Law Enforcement Agency (NDLEA)
2. Nigeria Secretary and Civil Defense Corp (NSCDC)
3. Nigerian Immigration Service (NIS)
4. Economic and Financial Crimes Commission (EFCC)
5. Federal Fire Service
6. Central Bank of Nigeria (CBN)
7. Federal Inland Revenue Service (FRIS)
8. Federal Industrial Court
9. Nagerian Financial Intelligence Unit (NFIU)
10. Nigerian Export-Import Bank Bank (NEXIM)
11. Independent Currupt Practices and tier related Offices Commission (ICPC)
12. Nigeria Correctional Services.
Haka zalika a fannin taimakawa matasa su zamo masu dogaro dakansu Abubakar Malami bayada na biyu inda ya ɗauki nauyin matasa kimanin dubu biyar (5000) koyon sanaoi hannu daban daban, goma sha biyar ƴan asali Jihar Kebbi domin Hukuma NIGCOMSAT ta koya masu harkar VSAT
Abubakar Malami ya samar aƙalla mutanen karkara da basu gaza 3,000 ba aikin Special Public Works (SPW) na NDE
Abubakar Malami ya samarwa matasa da basu gaza 45 ba aiki Graduate Attachment Program (GAP) na NDE
Abubakar Malami ya ɗauki nauyin mutum Talatin (30) domin Hukumar NITDA horar su sanin makamar aikin jarida.
Hakazalika akwai dimbin matasa ƴan asali Jihar Kebbi dake aiki a masana’antun Abubakar Malami da suka hada da
1. Rayhan Model Academy
2. Rayhan Hotels
3. Rayhan Mall
4. Rayhan Radio.
Ahmad Usman Mairukubta.